Title : TAMBAYA TA 1
»»»»»»»»»»»»»»
ASalamu alaikum, Allah ya sakawa malam da alkhairi.ina tambaya idan mutum zaiyi layya ance bazai yi aski ba ko yankan farce.shin malam da zarar ranar sallah tayi zanyi? ko sai an sakko daga idi? ko sai bayan nayi
yanka? wanne ne daidai?.
( daga ALI GURAJI KCK)
AMSA
»»»»»
Eh kamar yadda Annabi (saww) ya bayyana acikin ingantaccen hadisin, cewa yayi:
"Idan watan Zhul-Hajj ya kama, duk wanda yake da niyyar yin Layya kar yayi aski ko yankan farce har sai bayan ya yanka abin yankanshi"
Don haka sai bayan ka yanka abin yankanka.
(WALLAHU A'ALAM)
Description :