ILLAR MACE TA SAKA HOTO A PROFILE ( dp )
Yan uwana mata muji tsoron Allah mu sani
addinin musulunci ya mana gata ya kyautata
mana rayuwar, mu kuma ya kamata mu
karbi wannan kyautatawa da musulunci yaxo
mana da ita.
Wadannan hanyoyin sadarwan da yanxu aka
kawo mana wlh illar su tafi amfanin su yawa
musamman ga yan mata da samari, amma
duk da haka akwai wadanda suka kebance
kansu suka dauki wannan hanyar hanyar
da'awah a garesu, muna musu addu'ar Allah
ya saka musu da alheri.
Idan kika saka hotonki a profile baki san
adadin maxan da xasu gani, ba wani xai iya
yin savin a wayar shi yaje ya bata hoton ya
bata miki suna wanda Allah kadai yasan iya
inda hoton ki xai tsaya.
Wani mutumin banxa ne kina chattin dashi
ne kawai amma baki san halinshi ba. muna
gani yanda a fcbk suke yiwa yan mata wlknc
su rubuta a jikin
hoton budurwa IN DA ME SONTA YAMIN
MAGANA, yanxu idan wani dan uwanki yaga
wannan hoton ko ke kanki kika gani wane
irin bakin ciki xaki ji.
Idan har ke me shawa'awar saka
hotonki a profile ne to ki saka hoto me
mutunci wanda rashin sakawan ma shi yafi
alheri
Galibi hoton da muke sakawa wlh basu dace
ba wata xaka ga ta saka hoto kirjinta a waje
tayi dinkin banxa wanda ko yayanta bai dace
yaga wannan hoton ba amma sai ta sakawa
katti suna gani
Wata kuma tsayuwar da xata yi a hoton ma
kanshi bai dace ba, wata sai ta kwankwatsa
kwalliya yanda kasan aljana sannan ta dauki
hoton kuma ta saka a profile.
Me xai hana samari ba xasu rinka shiga wani
hali ba, kuma ko shedanun mata ne suka ga
hotonki suka ga kin musu daga nan xasu fara
bibiyar ki gashi nan yanxu yanda abubuwan
barna suke kara yawaita a social ntwrk.
Wlh akwa wacce sanadiyyar saka hoto a
profile auranta ya mutu mijinne yaga hoton a
fcbk wani yana cewa ga matar da xai aura
Wata kuma kaxafi aka mata yan lesbian grp
ne suka dauki hotonta aka canja mata kayan
jikinta aka hada hotonta dana wata yar
lesbian din suka rinka watsa hoton suna cewa
ga wadannan xasuyi aure.
Har hoto ya iso gareta tayita kuka wanda
kukan ba amfani
Wata tana saka hoto a dp ne saboda a gani
ace tayi kyau nasan in an yabi mutum yana
jin dadi amma me xai hana in kinyi kwalliyar
ki ki dauki hoton ki turawa grp dinku na
mata xalla, ko grps din skull dinku tunda
nasan baxaki rasaba in sukace kinyi kyau ke
kuma shikenan kinji dadi hankalin ki ya
kwanta.
Wanda wannan dinma barinshi shi yafi alheri
wlh wata a grp din maxa da mata take tura
hotonta kuma tayi kwalliya, ko batayi
kwalliya ba bai daceba balle kuma tayi.
Kwalliyan nan sai da Allah ya fada mana
iyakar wadanda xasuga kwalliyan mu su 12,
ne in dai kika bari,wani ya gani wanda baya
cikin 12 din nan to ya kalli masifa ke kuma
kinyi kwalliya a bala'i kije ki duba ( suratun
nurr shafi na 4 aya ta 31 ).
A wata ayar kuma Allah ya kirayi manxonsa
yace ....( YAA'AYYUHANNABIYYU QULLI
AZAWAAJIKA WA BANAATIKA WANI SAA'IL
MUUMININA YUDNIINA ALAYHINNA MIN
JALABII BIHINNN.)
ke hadaki da matan manxon Allah a hadaki
da yayan manxon Allah a taraki da mata
muminai na duniya abu,daya fa Allah yake so
shine ki sauje lullubin ki
Daga karshe yan uwa ina mana nasiha cewa
muji tsoron Allah, wlh duk wata masifar da
samari suka fada yanxu mafi aksari yan mata
ke jawo musu.
Muma muji tsoron Allah mu sani duk abun
da muka aikata akwai ranar da xamu tashi da
aikin mu maqale a wuyan mu Allah yace ...
( WAKULLA INSANIN ALZAMNAAHU
DHAA'IRAHUU FII UNUQIH WANUKH RIJU
LAHUU YAUMAL QIYAAMATI KITAABAYN
YALQEEHU MANSHUURAA. IQRA'A
KITAABAKA KAFEE BINAFSIKAL YAUMA
ALAIKA HASIIBA.)
Sannan shi kuma littafin Allah ya fada mana,
LAAYUGHADIRU SWAGHIIRATANW WALAA
KABIIRATAN ILLA AHSWEEHAA.
Wlh duk abun da kika aikata xaki karanta
kayanki, duk wani namijin da kika yi
sanadiyyar lalacewar sa kema da naki
xunubin.
Idan akwai wacce na bata wa rai a cikin
rubutuna dan Allah ta yafe min.
By bansubaba
Title : ILLAR MACE TA SAKA POTO A PROFILE
Description : ILLAR MACE TA SAKA HOTO A PROFILE ( dp ) Yan uwana mata muji tsoron Allah mu sani addinin musulunci ya mana gata ya kyautata mana rayuwar...