...Ci gaba da karatun littafin...
♡SIRRORIN MIJI DA MATA♡***
Na
ABU MANAR ALQASIM
{2014}.
.
Darasi na 44.
.
☆** 📝ABUBUWA MASU MUHIMMANCI.👇🏻**☆
.
.
☆** Ku iyaye ku sake duba wasu abubuwa masu matuqar mahimmancin gaske, daidai da abin da Ubangiji S.W.T. ya fadi a (Suratun Nisaa Aya ta 9)
ﻭﻟﻴﺨﺶ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻟﻮ ﺗﺮﻛﻮﺍ ﻣﻦ ﺧﻠﻔﻬﻢ ﺫﺭﻳﺔ ﺿﻌﺎﻓﺎ ﺧﺎﻓﻮﺍ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﻓﻠﻴﺘﻘﻮﺍ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻟﻴﻘﻮﻟﻮﺍ ﻗﻮﻻ ﺳﺪﻳﺪﺍ .
[Lallai wadan da da za su rasu su bar zuriyarsu ('ya'yansu) cikin rauni (qanana) za su ji musu tsoro (na shiga wani irin hali).
.
☆** Su kiyaya, lallai su ji tsoron Allah, haqiqa su fadi magana irin wace ta dace] Yara suna buqatar komai ne daga iyayensu masamman 'ya'ya mata, qauna ba ta nufin ku riqa jiyar da su dadi albashi in suka rabu da ku su shiga wani hali na qunci, kamar yadda ba ta nufin ku wahalar da su, amma ku nuna musu komai na rayuwa ta yadda ba za su sha wahala nan gaba ba, ku yi tunanin cewa ana iya samun mutuwa, ko canjin rayuwa, ko saki, ko wani lamari wanda zai iya sauya sifar rayuwar, idan 'ya'yanku suka koyi yadda za su fuskanci rayuwa tabbas ba za su sha wahala ba, tarbiyya ba ta nufin karatun addini kawai, tarbiyya a wajen 'ya mace tana da fadi sosai.***
.
☆** Tun tana qaramar yarinya dole ta san yadda ake tsara daki, wuraren da ya kamata a ajiye takalma, kwanoni, riguna, kayan kwalliya da su tsintsiya da sauransu, dole ne uwa ta riqa gaya wa 'ya'yanta mata, qanana, mahimmancin tsafta da yadda ake shirya dakin zama da na kwanciya, yarinya ta san wuraren da ake ajiye komai, da lokutan da ake tsaftace ko'ina, hatta masu rayuwa a maraya.***
.
☆** Wadan da suke da abin hannunsu su ma dole su ji tsoron Allah su riqa tarbiyyantar da 'ya'yansu tun suna qanana, yaran su saba da share daki duk lokacin da ya yi datti, da aji ye komai a mahallinsa, dole su iya wanke kayan sakawansu duk da cewa akwai halin kai wa wankau, wannan domin tarbiyyantar da su ne sabo da Allah ne kadai ya san gaba, ya zama dole uwa ta bar 'ya'yanta mata su riqa wanke-wanken kwanonin abinci ko da kuwa suna da 'yan aiki, wannan ba qasqantarwa ba ce, sauke nauyin da Allah ya daura mata ne na bai wa 'ya'yanta mata cikakkiyar tarbiyya.***
.
☆** Mata masu aiki a cikin gida za su riqa musayar aiki tare da yaranki a kowani lokaci, hatta wanke dakunan wanka da na ba-haya da share tsakar gida, da goge qofofi da tagogi, za su riqa yin canji tsakaninsu da ma'aikatan gidan, wannan ba wai kina rage wa ma'aikatan aiki ba ne, a'a suna koya wa 'ya'yanki ne yadda za su iya rayuwa da kowani irin yanayin da suka sami kansu in kina da rai ko ba ki, in sun yi aure ko rabuwar aurenki (Allah ya kyauta) ta faru, kar ki ce to yanzu sun iya shi kenan, a'a wannan zai ci gaba ne har zuwa aure yadda za su shiga dakin mazajensu da wannan cikakkiyar tarbiyya da kika ba su.***
.
☆** Ba shakka masu gidansu za su ji dadin zama da su, sabo da rashin ganda da qiwa, da tsai da komai yadda ya dace gwargwadon tarbiyya ta qwarai da kika yi musu.***
.
☆** Zancen dafa abinci kuwa yarinyarki qarama za ta fara zuba gishiri da magi gwargwadon yadda kika di ba kika zuba mata a hannu, don ta zuba a cikin abinci, wannan zai ci gaba, har a kai matsayin da za ta riqa diba tana zubawa da hannunta, daganan sai nau'o'in abinci da yadda ake hada su, da lokutan yin su, uwa tana koyar da 'ya'yanta qanana duk wasu fannoni na abinci tun ba su yi wayau ba.***
.
☆** Yarinya takan kai matsayin budurwa da sabo da dafa duk wani irin nau'I na abinci, tun da ita take yin na gidansu sai dai uwar da sauran 'yan uwa su riqa taimakawa kawai, a nan uwa za ta riqa koya musu dabarun yin abinci da yadda zai yi dadi koda ba a kashe kudi mai yawa ba, uwa za ta riqa gaya musu yadda za su tafiyar da kicinsu in har bai kai na gidansu ba, tare da sanar da su juyawar rayuwa, misali ta gaya musu ita ma ga yadda take kafin maigidan ya zama yadda yake yanzu.***
.
☆** Wadannan abubuwa duk za su fara ne tun 'ya'ya mata suna qanana shekara 4, uwa ta ji tsoron Allah tare da ganin ta bai wa 'yarta duk wata tarbiyya ta riqe gida, misalin wanke takalma, da gugan kaya da gyara kai, ta wajen yin wanka sau biyu a rana, da iya kwalliya kala-kala, ba laifi uwar ta riqa gaya mata "Kin yi kyau" ko "Nan bai yi ba" ko "ya kamata ki yi kaza" ta riqa gaya mata mahimmancin yin ado ga miji tare da mahimmancin 6oye shi a gaban wanda ba mijinta ba.***
.
☆** Duk wasu dabi'u na cikin gida, uwa ta riqa duban cewa ba dole ba ne 'yarta ta sami rayuwa irin na gidan ubanta, ko da kuwa za ta samun ta sani cewa umurni ne daga Allah da ya wajaba a kanta na tarbiyyantar da 'ya'yanta, wannan 6angaren aiki kenan saura 6angaren dabi'u da ibada.***
.
.
Zan dakata anan sai kuma darasi nagaba in shaa Allah.
.
.
Title : SIRRIN MIJI DA MATA
Description : ...Ci gaba da karatun littafin... ♡SIRRORIN MIJI DA MATA♡*** Na ABU MANAR ALQASIM ...