WANI MAI HIKMA NA CEWA :
Kasala tanemi ta tsai da ni sallar 1 bisa 3 na qarshen dare sai na samu abin mamaki acikin ta !!
1- Lallai sallar Farillah ladanin dake kiranta mutumne 'dan adam, amma sallar 1 bisa 3 na qarshen dare Mahaliccin 'dan adam ke kiranta.
2- Ita sallar Farillah dukkan nin mutane najin ladanin dake kiranta, amma ita sallar 1 bisa 3 na qarshen dare kadanne daga cikin mutane suke jin ajikinsu ana kiranta.
3- Ita sallar Farillah kira
zuwa sallar shine (Hayya alas salat, Hayya alal falah), amma sallar 1 bisa 3 na qarshen dare kiranta Allah ne da kanshi yake cewa :- (Shin akwai mai roqona na biya mai buqatunsa..).
4- Ita sallar Farillah mafi yawan mutane na yinta, amma ita sallar 1 bisa 3 na qarshen dare sai wanda Allah ya zaba daga cikin bayinsa masu imani suke yinta.
5- Ita sallar Farillah wasu suna yintane dan kar ace basayi, amma ita sallar 1 bisa 3 na qarshen dare bamasu yinta sai aboye saboda neman yardar Allah.
6- Ita sallar Farillah da yawa na yinta ne tare da tinanin shagulgulan duniya da wasiwasin shaidan, amma ita sallar 1 bisa 3 na qarshen dare dayawa na yintane dan yankewa tinanin duniya saboda gina gidan lahira.
7- Ita sallar Farillah wasu na zuwantane domin a hadu su tattauna, amma ita sallar 1 bisa 3 na qarshen dare da yawa na yintane domin kusantar Allah SWA da gayawa Allah abinda ke damun bawa tare da roqon Allah SWA.
8- Ita sallar Farillah ba lallai bane idan aka roqi Allah ya amsa, amma ita sallar 1 bisa 3 na qarshen dare Allah yayiwa bayinsa alqawarin amsa musu idan suka roqeshi.
Daga qarshe ita sallar 1 bisa 3 na qarshen dare babu wanda ke dace da yinta sai wanda Allah SAW yakeso yaji matsalolin shi, kuma yaji abinda ke damun sa da abinda yakai kuka gareshi;
Madalla gawanda ya samu dagewa gurin kiran Ubangiji Mabuwayi kuma Madaukaki sarki domin tsayuwa agabansa da kai kokensa ga Allah tare ni'imtuwa gurin kebantuwa gareshi.
Karka Haramtawa kanka da waninka wannan ni'ima, wata qila idan ka turawa 'yan uwa zaka qarfafama wani tsayuwar dare.
Title : WANI MAI HIKIMA NACEW
Description : WANI MAI HIKMA NA CEWA : Kasala tanemi ta tsai da ni sallar 1 bisa 3 na qarshen dare sai na samu abin mamaki acikin ta !! 1- Lallai sall...