⚱MU KOYI IBADA⚱
➖➖➖➖➖➖
FITOWA TA ARBA'IN
✒ SALLAH
➖➖➖
Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jinkai
KIRAN SALLAH DA IQAMA
➖➖➖➖➖➖➖➖➖
KIRAN SALLAH: Shine Sanar da Shigar Lokacin Sallah da Wasu Lafuzza Ke6antattu.
HUKUNCIN KIRAN SALLAH
➖➖➖➖➖➖➖➖➖
Kiran Sallah Wajibine Na Kifaya (Wato Wani Na Daukewa Wani) Akan Mutanen Birane da Kuma Mutanen Kauyuka; Manzon Allah(ﷺ) Yace: {Idan Lokacin Sallah Yayi, To Dayanku Yayi Muku Kiran Salla; Kuma Mafi Girma a Cikinku Yayi Muku Limanci}¹.
Kuma An Sunnantawa Matafiyi da Makiwaci Yin Kiran Sallah Domin Manzon Allah(ﷺ) Yana Cewa: {Idan Ka Kasance zaka Kira Sallah a Cikin Dabbobinka ko a Kauyenka, To Ka 'Daga Muryarka; Domin Babu Wani Daga Cikin Aljanu Ko Mutane Ko Wani Abu Na Daban da Sautin Kiran Sallar Zai Isa Zuwa Gareshi, Face Yayi Masa Shaida a Ranar Kiyama}².
SIGAR KIRAN SALLAH
➖➖➖➖➖➖➖➖
Sigar Kiran Sallah Kamar Yanda Manzon Allah(ﷺ) Ya Karantar da Abi-Mahzurah Shine:
{Allahu Akbar, Allahu Akbar}
{Ash'hadu An Lã'ilãha Illallah, Ash'hadu An Lã'ilãha Illallah}
{Ash'hadu Anna Muhammadar Rasulullah, Ash'hadu Anna Muhammadar Rasulullah}
{Hayya Alas Salah, Hayya Alas Salah}
{Hayya Alal Falãh, Hayya Alal Falãh}
Idan Kiran Sallar Asubah ce Sai Yace: {As-Salãtu Khairun Minan Naum, As-Salatu Khairun Minan Naum}.
{Allahu Akbar, Allahu Akbar}
{Lã'ilãha Illallah}.
___________________________________
1. Bukhari (1/162, 163), Muslim (292) Kitabul Masajid.
2. Rabi'i bn Habib Cikin Musnad Dinsa (1/37).
**************************************
Anan Zan Dakata Sai Mun Hadu a Fitowa ta Gaba
سبحانك اللهم وبحمدك اشهد ان لااله الا انت استغفرك واتوب اليك
Title : MUKOYI IBADA
Description : ⚱MU KOYI IBADA⚱ ➖➖➖➖➖➖ FITOWA TA ARBA'IN ✒ SALLAH ...